<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Yara, Mu Tashi da Murna Mai Yawa LW77</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yara, mu tashi da murna mai yawa,
 Zo, za mu gai da Mai Cetonmu yau,
 Ga shi a kwance, jariri ƙanƙane,
 Tare da shanu a Baitalahmi can.

[V2]
 2) Taron mala'iku, ga su a Sama,
 Waƙa mai daɗi kuwa su ke ta yi,
 &quot;Yaba ga Allah, a duniya salama.&quot;
 Zance mai faranta zuciya ne.

[V3]
 3) Hasken tauraron nan ne suka gani,
 Shehunan gabas sun tashi, sun zo.
 Kayan zinariya ne suka kawo,
 Duk suka zuba gabansa kyauta.

[V4]
 4) Yesu mai sonmu, mu ƴaƴanka kuma,
 Ga mu, mun taru da gaisuwarmu.
 Lubban ka murru ba su ne muka kawo ba,
 Kayan zinariya ba mu da su.

[V5]
 5) Mu dai, ga kayan da mu za mu kawo,
 Ƙarfinmu, ƙaunarmu, zuciya da rai,
 Duk mu ke ba ka, jariri, Mai Ceto,
 Kai ne masoyinmu har abada.</lyrics>
<hymn_number>77</hymn_number>
</song>